in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nada kanal Zida a matsayin sabon faraministan Burkina Faso
2014-11-20 13:52:02 cri

Sabon shugaban rikon kwarya na kasar Burkina Faso, Michel Kafando ya nada Laftanal kanal, Isaac Yacouba Zida a matsayin sabon faraminstan kasar Burkina Faso a ranar Labara, in ji mataimakin sakatare janar din kwamitin ministoci, Thiery Alain Ouattara. A tsawon makwanni uku da suka gabata, mista Zida ya kasance shugaban wuci gadi na soja kafin ya mika mulki ga fararen hula. Bayan wannan nadi, mista Zida wanda ya kori darektocin kamfanonin gwamnati biyu kafin ya dakatar da kwamitocin wakilan jama'a, zai kafa gwamnatinsa. Ana jiran taron ministocin sabuwar gwamnatin wucin gadi a ranar Asabar mai zuwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China