Ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian a ranar Laraban nan ya sanar da cewar, za'a tura karin jiragen saman yaki guda 6 a kasar Jordan don su karfafa kokarin da ake yi na dakile ayyukan kungiyar IS a Iraqi. Ya yi bayanin cewa, tun da farko akwai guda 9 a daular kasashen Larabawa, yanzu za'a aika da 6 a kasar Jordan don ba da taimako wajen ganin an dakile ayyukan wannan kungiya.
Jean-Yves Le Drian ya ce, wannan kokarin ya biyo bayan hadin kan da sauran kasashe ne ta bangaren hari ta sama wanda a ciki Faransa take jagoranta.
Tun da farko a ranar Laraban, jiragen saman yakin guda 2 da wassu jiragen sama na kasashen hadin gwiwwa sun kai hari a kan wassu wuraren da ake zargin kungiyar na amfani da su a garin Kirkuk dake arewacin Iraqi domin dakushe karfinsu wajen yaki da sojojin Iraqin da IS.
A watan Satumba, Faransa ta shiga hadin kan kasashen da Amurka ke jagoranta wajen yaki da kungiyar ta IS a Iraqi da ta kwace manyan garuruwa, take kuma barazana ga tsaron yankin baki daya. (Fatimah)