Rahotanni daga Libya na cewa, sojojin kasar sun gagadi mazauna birnin Tripoli da su bar wuraren da sojojin suka yi niyyar kaddamar da hare-hare yayin da suke kokarin kwato birnin daga hannun 'yan tawaye.
Wata sanarwa da sojojin suka bayar ta gargadi al'umma da su kaurewa wurare kamar sansanonin soja, hedkwatocinsu da wuraren adana makamai don gudun abin da zai biyo baya. kuma sojojin Libya ba za su dauki alhakin duk wata barna ba.
Birnin Tripoli dai ya fada hannun 'yan tawaye ne tun a watan Agustan da ya gabata, lokacin da kungiyoyin da ba sa ga maciji da juna suka kaddamar da hare-haren kokarin kwace iko da birnin.
Wannan ya sa, a ranar Asabar din da ta gabata, sojojin suka ayyana cewa, za su dauki matakan kwato birnin daga hannun mayakan.
Tun lokacin da aka hambarar da tsohon shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011 ne kasar Libya ta fuskanci tashin hankali. (Ibrahim)