in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe filin saukar jirgin saman Libya bayan musayar wuta
2014-11-17 10:57:27 cri

An rufe filin saukar jirgin sama na Tripoli, babban birnin kasar Libya, a sakamakon barkewar musayar wuta a zagayen filin jirgin saman a jiya Lahadi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar Libya, LANA ya bayyana.

Shugaban sufuri na Tripoli Hakim Ahmed al-Shwehdi ya ce, an dakatar da daukacin zirga-zirgar sauka da tashin jiragen sama daga filin jirgin sama na Mitiga, har sai bayan an girka matakan tsaro.

Al-Shwehdi ya kara da cewar, an kashe masu gadi guda biyu a lokacin dauki ba dadi na musayar wuta da aka yi a kusa da kofar shiga filin jirgin saman na Mitiga.

Kawo ya zuwa yanzu, babu wanda ya san wadanda suka kai harin da kuma dalilin da ya sa suka aiwatar da farmakin.

Ana amfani da tsohon filin jirgin saman sojoji dake Mitiga domin jigilar jirage na jama'a, bayan mummunar arangamar da aka yi tsakanin 'yan tsageran musulunci da kuma masu neman kafa gwamnati marasa nasaba da addini a filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Tripoli a watan Yulin da ya gabata.

Kasar Libya ta fuskanci karuwar tashin hankali tun daga watan Mayu a yayin wani kazamin artabu tsakanin dakarun Islama da dakarun kafa gwmanati maras nasaba da addini.

Kawo ya zuwa yanzu, ana ci gaba da samun barkewar munanar arangama a kusa da garuruwan Tripoli, Benghazi da Gharyan. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China