in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a tsagaita wuta na awoyi 12 a birnin Benghazi na Libya
2014-11-20 14:18:17 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar Libya UNSMIL ta yi shelar cewar, kungioyoyi dabam-dabam wadanda ba su jituwa da juna, a rikicin da ake yi a Benghazi dake kasar Libya a yanzu sun amince da tsagaita wuta na awoyi 12, domin samun sukunin shigar da kayayyakin agaji a wuraren da ake rikicin.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya ce, yarjejeniyar wacce sojojin wanzar da zman lafiya na MDD suka zama masu shiga tsakani, ta fara aiki tun daga karfe 7 na safiyar agogon kasar ta Libya zuwa karfe 7 na dare, tawagar ta MDD ta kuma bukaci dukanin bangarorin da su yi biyayya ga dukanin sharuddan wannan 'yarjejeniya.

Kamar dai yadda dukanin bangarorin suka amince, kungiyar agaji ta Red Crescent ta kasar za ta dauke fararen hula daga wuraren da rikicin ya shafa tare kuma da dauke gawawwki da kuma taimakawa wajen kwashe bayan gari da sauran datti.

Tawagar wanzar da zaman lafiya na mai fatan farara hula za su kara samo abincin da za su adana da kuma kulawa da wadanda suka sami rauni.

Tun dai bayan da aka hambaras da gwamnatin tsohon shugaban kasar marigayi Muammar Gaddafi, sai rikici ya watsu a cikin kasar.

Wasu alkalumman kididdiga na hukumar 'yan gudun hijira ta MDD UNHCR sun nuna cewar, a kalla mutane kimanin 106, 420 ne suka tsere daga kasar ta Libya a cikin watan Oktoba.

Kididdigar ta nuna cewar, wasu mutane 393,400 sun rasa muhallansu a sakamaokn rikicin. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China