Kasar Iran da wasu manyan kasashen duniya sun tattauna a kan shirin nukiliya na Iran, to amma kuma har yanzu akwai banbance-banbancen ra'ayi tsakanin kasar ta Iran da kasashen yammaci.
Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya shaidawa 'yan jarida cewar, za'a ci gaba da tattaunawa, kuma tattaunawar da aka yi a ranar Lahadi ta yi matukar amfani.
To amma tun farko, wasu manyan jami'an diplomasiyya na Amurka da Britaniya sun bayyana cewar, tattaunawar da aka yi a kan rashin daidaiton da aka samu a kan shirin makamashin nukiliya na Iran, a bisa dukkan alamu, ba za a iya samu wata nasara ba a daidai lokacin da aka diba, kila za a cimma yarjejeniya a cikin mako guda mai zuwa. (Suwaiba)