Kasar Aljeriya, ta bakin ministan harkokin wajenta, Ramtane Lamamra, tana watsi a halin yanzu da duk wani matakin tura sojoji a kasar Libya, tare da jaddada cewa, yanzu maganar ita ce bullo da wata hanyar sulhu tsakanin 'yan kasar Libya domin fitar da kasar daga cikin rikicin dake fama da shi a halin yanzu.
Babu wani shirin tura sojoji a Libya da aka tsai da a halin yanzu, amma babbar magana a halin yanzu ita ce hada kan 'yan kasar Libya bisa turbar shawarwarin tsakanin 'yan kasa, sassantawa da kuma karfafa karfin hukumomin kasa bisa tsarin demokuradiya, in ji mista Lamamra a ranar Laraba a yayin wani zaman taro kan matsayin mata a cikin hadin kan iyali da zaman karkon al'umma.
Wannan sanarwa ta zo a matsayin mai da martani ga kalaman ministan tsaron kasar Faransa, Jean-Yves Le Drian da ya bayyana a cikin wata hirar da ta fito a ranar Talata a cikin jaridar Figaro ta kasar Faransa cewa, ya kamata mu dauki matakai kan Libya, kuma hakan na gudana yadda ya kamata tare da hadin gwiwa tare da kasar Aljeriya, wadda ta kasance wata muhimmiyyar kasa mai ruwa da tsaki a wannan shiyya. Game da wadannan kalamai, shugaban diplomasiyyar kasar Aljeriya, ya bayyana cewa, bai yi tsammanin wadannan kalamai ba su fito daga bakin jami'in kasar Faransa ba. Har kullum game da batun kasar Libya, mista Lamamra ya sake tunatar da matsayin kasar Aljeriya dake bisa tushen kaucewa yin duk wani shisshigi a cikin harkokin cikin gida na sauran kasashe. (Maman Ada)