Annobar zazzabin cutar Ebola ta kashe mutane 5 daga cikin mutane 15 da aka tabbatar dauke da kwayoyin wannan cuta a kasar Saliyo, in ji ma'aikatar kiwon lafiyar kasar a ranar Litinin.
Har zuwa wannan lokaci, mun tabbatar da cewa, mutane goma sha biyar suka kamu da cutar Ebola daga cikin mutane talatin da shida da ake zaton da suna fama da bala'in, kuma daga wadannan mutane goma sha biyar, mutane biyar sun mutu, in ji mista Idriss Tunis, darektan watsa labarai na ma'aikatar kiwon lafiyar kasar a yayin wani taron manem labarai.
Jami'in ya jaddada cewa, daga cikin mutanen biyar da suka mutu, uku sun mutu a asibiti a yayin da biyun suka mutu a cikin gida.
Wadannan mutane goma sha biyar sun fito daga gundumar Kaikalun, sha hudu daga Kissy Teng, kana dayan daga Daru dake gabashin Saliyo.
Mun kara ayyukan fadakarwa da ilmantar da mutane, ta yadda za su fahimci babbar illar wannan annobar, har za su iyar kasancewa cikin shirin ko ta kwana domin sanya ido da rigakafin yaduwar wannan cuta, in ji mista Tunis. (Maman Ada)