Wata kotu a Libya ta dage sauraron shari'ar jami'an da suka yi aiki da tsohon shugaban kasar Mu'ammar Ghaddafi a ranar Lahadin nan zuwa Lahadi biyu na sama wato 16 ga watan da muke ciki.
Shari'ar ta jami'ai 23 ana yin ta ne a gidan yarin al-Hadba dake cikin birnin Tripoli. Sai dai wanda ake zargi na farko Saif Al-Ghaddafi bai bayyana a lokacin shari'ar ba bisa ga dalilan fasahar na'ura da aka samu jinkirin dauko shi daga gidan yarin Zintan inda yake tsare.
Mai shari'ar don haka a lokacin shawarwari da sauran alkalai ya dage sauraron karar zuwa 16 ga watan Nuwamba.
Su dai wadanda ake zargin, ana tuhumar su ne da laifuffuka da dama da suka hada da laifin mara wa tsohuwar gwamnati baya, abin da ya janyo boren shekara ta 2011, cin hanci da rashawa da kudaden gwamnati, kisan kare dangi da kuma ingiza mutane su yi fyade, tare da ba da iznin a yi ta karbi kan bayin Allah da ba su ji ba ba su gani ba lokacin da suke zanga-zanga. Haka kuma ana zargin su da shatan makamai da kuma kafa kungiyar mayaka da rundunoni, kafa kungiyar masu dauke da makamai tare da sata da fashe gidajen jama'a suna diban ganima. (Fatimah)