Kungiyoyin fararen hula, da jam'iyyun siyasa, tare da wakilan rundunar soji a Burkina Faso, sun mika sunayen mutane 3, domin zabar guda da zai jagoranci gwamnatin rikon kwaryar kasar, ya zuwa lokacin da za a gudanar da babban zabe.
Rahotanni sun bayyana cewa, sassan masu ruwa da tsakin sun kai ga mika sunayen mutanen 3 ga shugaban wucin gadin kasar na soji ne, bayan kammala taron da suka gudanar a jiya Lahadi.
Mutanen da aka mika sunayen na su dai sun hada da Bishop Paul Ouedraogo, babban malamin majami'ar Bobo-Dioulasso, da tsohuwar ministar kasar uwargida Josephine Ouedraogo, da kuma tsohon gwamnan babban bankin yammacin Afirka Justin Damo Barro.
Ana kuma sa ran nan da dan lokaci, gwamnatin rikon kwaryar kasar karkashin jagorancin Laftana Kanar Isaac Zida, za ta bayyana wanda ta amince da shi cikin mutanen 3. (Saminu)