Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, ya kaddamar da wani katafaren aiki na fadada tashar wutar lantarki ta kudancin Kariba, wacce ita ce tasha ta biyu mafi girma a kasar.
Gwmnatin ta Zimbabwe ta bayar da kwangilar gudanar da wannan aikin ne ga wani babban kamfanin gine-gine na kasar Sin, Sino-Hydro.
Shi dai kamfanin Sino-Hydro, zai kara gina wasu injuna biyu na samar da wutar lantarki kuma kowanensu zai dinga samar da karin megawatts 150, na karfin wutar lantarki a ko wace shekara ga tashar samar da wutar lantarkin ta Kariba, wacce ke da injuna 6, wadanda kowanensu ke samar da megawatt 125, na karfin wutar lantarki.
Wannan aiki na fadada tashar wutar lantarkin ta Kariba zai haifar da karin karfin wutar lantarki a kasar da kashi 1 bisa 4 a cikin shekaru fiye da 3, hakan na nufin Zimbabwen ta kusa kawo karshen matsalar karancin wutar lantarki da kasar ke fama da ita.
Wannan aikin dai zai ci zunzurutun kudi, har dalar Amurka miliyan 533, kuma daga cikin wannan adadi, dala miliyan dari 319, bankin kasar Sin na shigowa da fitar da kaya ne zai samar da wadannan kudade a matsayin bashi mai sauki ga kasar ta Zimbabwe.
Jakadan kasar Sin a Zimbabwe, Lin Lin ya bayyana cewar, kasar ta Sin ta kuma baiwa kasar ta Zimbabwe kyautar dalar Amurka miliyan 20 da kuma bashin dalar Amurka miliyan 218 ga kamfanin waya na kasar ta Zimbabwe. (Suwaiba)