in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aka kashe mayakan IS 59 a cikin gumurzu da hare-haren sama
2014-10-16 10:57:25 cri

Aka kashe mayakan kasar musulunci ta IS 59 a ranar Laraba a cikin gumurzu tare da sojojin kasar Iraki, da kuma luguden wuta ta jiragen yaki kan sansanoninsu dake Iraki, in ji majiyoyin tsaro. A gundumar Diyala, sojojin Iraki tare da tallafin mayakan sa kai na Shi'a sun kai wani samame kan sansanonin IS dake yankin Mansouriyah, mai tazarar kilomita kusan dari daga arewa maso gabashin birnin Bagadaza. A yayin wadannan gumurzu, sojojin Iraki sun kashe a kalla mayakan IS guda 12, in ji wata majiyar tsaron gundumar da ta bukaci a sakaya sunanta a yayin hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Haka kuma, a Diyala, sojojin Iraki sun ja daga da mayakan IS a Albu-Talha dake arewa maso gabashin gundumar, inda aka kashe mayakan IS goma sha biyar, tare da lalata motocinsu shida, in ji wannan majiya.

A karshe, a gundumar Anbar, sojojin Iraki tare da taimakon wani jirgin yaki na kawancen da Amurka ke jagoranta sun kori a ranar Laraba da wani harin wasu mayakan IS da suka yi yunkurin kwace garin Al-Baghdadi, dake kimanin kilomita 200 daga arewa maso yammacin Bagadaza, in ji wata majiyar tsaron gundumar da ta sakaya sunanta a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, tare da nuna cewa, aka kashe a kalla mayakan IS goma sha uku, tare da lallata motocinsu a cikin gumurzu da hare-haren sama. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China