in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Burkina Faso sun saki kan kundin wucin gadi
2014-11-14 12:58:55 cri

Kungiyoyin fararen hula, jam'iyyun siyasa da rundunar sojojin kasar Burkina Faso sun warware rashin jituwar dake tsakaninsu kan batun kundin wucin gadi a ranar Alhamis, lamarin da ya bude hanyar yin shawarwari tare da fararen hula domin kammala kundin. Shirin kundin wucin gadi da fararen hula suka tsara ya samu amincewar sojojin kasar a ranar Laraba. Shawarwarin sojojin kasar dake hannun riga da na fararen hula sun shafi soke majalisar dokokin rikon kwarya, soke kwamitin tsaron kasa da kwamitin sasanta 'yan kasa da gyare gyare. Haka kuma shawarwarin sojojin sun yi hasashen karfafa kwamitin rikon kwarya na kasa (CNT) da zai kasance da wani dandalin tuntubar juna da wani soja zai jagoranta.

A cikin shirin kundin wucin gadi na farko, kungiyoyin fararen hula sun tsai da farar hula a matsayin shugaban kwamitin, gwamnatin dake kunshe da ministoci 25 da majalisar dokokin rikon kwarya dake kunshe da 'yan majalisa 90, inda sojoji suke da kujera 10, kana tsohon kawance mai mulki kujeru 10, a yayin da sojoji suka ba da shawarar kafa majalisar dokokin rikon kwarya mai kunshe da mambobi 60, wato adawa kujeru 15, kungiyoyin fararen hula kujeru 15, sojoji kujeru 15 sannan tsohon kawancen dake mulki kujeru 15.

Sai dai a cewar kungiyoyin fararen hula, shawarwarin sojojin na da wata manufar dake boye da buri biyu, wato maido da tsohon iko ta hanyar aiki da tsoffin shugabannin a cikin mulkin wucin gadi da kuma kin canja kundin tsarin mulkin kasar.

Sojojin kasar da suka halarci wani kwamitin shawarwari a ranar Laraba tare da 'yan adawa, fararen hula da hukumomin addinai da na gargajiya, sun bayyana cewa, sun saki kan wasu batutuwa, amma kuma sun ce magana da karshe tana gare su.

Sojojin sun amince da shugaban majalisar dokokin rikon kwarya, shugaban kwamitin CNT ya kasance farar hulan da 'yan uwansa suka zaba, wanda kuma daga baya zai zabi faraministansa wanda shi kuma zai nada ministoci 25 na gwamnatinsa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China