Wani babban jami'in gwamnatin kasar Zambiya ya mai da martani ga kalaman da wani jami'in kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ya fitar dake cewa, kasar Zambiya ba ta shirya ba wajen yaki da cutar Ebola, in ji kamfanin dillancin labarai na Zambia Daily Mail.
A ranar Litinin, darektan WHO dake kula da rigakafin da sa ido kan cututtuka a cibiyar shiyyar Afrika, mista Francis Kasolo ya bayyana cewa, Zimbiya ba ta shirya ba wajen fuskantar Ebola dake afkawa kasashen dake gabashin Afrika.
Sai dai ministan kiwon lafiya na kasar, Joseph Kasonde ya bayyana cewa, wannan sanarwa ba ta da tushe da sabanin kalaman WHO, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar ta aiwatar da wasu matakan da suka dace domin killace da hana yaduwar wannan cuta mai kashewa.
A cewar mista Kasonde, ma'iakatarsa ta kafa wani rukunin kwararru da ya kaddamar da kamfen horar da fadakar a cikin manyan hanyoyin shigowa cikin kasar, har ma cikin manyan filayen jiragen sama hudu na kasar. (Maman Ada)