Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe dake shugabancin taron kungiyar cigaban kasashen kudancin Afrika (SADC), ya bayyana a kwanan nan cewa, zai kara ba da kwarin gwiwa ga masu zuba jarin kasar Sin wajen zuba kudi kan muhimman ayyuka a kudancin Afrika.
Mista Mugabe ya bayyana cewa, zai nemi taimakon Sin, musammun ma a fannin bunkasa gine-gine da kuma ayyukan kara zuba jari a wannan shiyya a yayin ziyarar aikin da zai kawo a nan kasar Sin.
A cewar wani rahoton kasa da kasa kan zuba jari na taron MDD na shekarar 2014 kan kasuwanci da cigaba (UNCTD), tattalin arzikin kungiyar SADC ya samu jarin da aka zuba kai tsaye daga kasashen waje da aka kiyasta shi zuwa dalar Amurka biliyan 13 a shekarar 2013, wanda ya haura bisa ga na shekarar 2000 wato dalar Amurka biliyan 4,5.
A kasar Zimbabwe, kasar Sin muhimmiyar kasa ce kawai da ta jima tana zuba jari a tsawon shekaru dama. Kamfanonin kasar Sin, daga cikinsu, kamfanin Sino-Hydro da ya zuba jari fiye da dalar Amurka biliyan 1,5 a bangaren ayyukan samar da wutar lantarki.
A cikin wata sanarwa da aka fitar bayan dandalin kwanaki biyu, an bayyana cewa, bunkasa cigaban kamfanoni zai kasance a tsakiyar tsarin jadawalin dunkulewar shiyyar SADC, kana wani kwamitin aiki na ministoci, an ba shi nauyin bullo wata dabara da wani jadawalin aikin bunkasa masana'antu. (Maman Ada)