in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta baiwa DRC taimakon kayayyaki da magunguna ton 17
2014-10-30 13:39:37 cri

Kasar Sin ta baiwa DRC-Congo kyautar ton 17 na magunguna da kayayyakin kariya daga kamuwa da annobar cutar Ebola dake kamari a gundumar Equateur dake arewcin kasar DRC-Congo, in ji kamfanin dillancin labarai na Xinhua a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Ndjili dake birnin Kinshasa. Bikin ba da taimakon ya gudana a filin jiragen saman Ndjili a gaban idon jami'in dake kula da harkokin ofishin jakadancin kasar Sin dake DRC, mista Chen Zhihong, da kuma ministar shari'ar DRC, madam Wivine Mumba dake wakiltar ministan kiwon lafiya. Wannan taimako darajarsa ta kai fiye da dalar Amurka dubu dari takwas kuma kai nauyin ton 17, kuma an yi jigilar wadannan kayayyaki da magunguna ta wani jirgin sama na musammun na gwamnatin kasar Sin, in ji Chen Zhihong, tare da nuna cewa, birnin Kinshana shi ne zangon farko na wannan jirgin sama, kuma zai isa daya bayan daya zuwa biranen Accra, Abidjan, Bamako, Bissau da kuma Cotonou, inda zai sauke irin wadannan kayayyaki da magunguna. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China