in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire na daidaita matsayin diplomaiyyarta a kasashen duniya
2014-01-21 09:41:25 cri

Kasar Cote d'Ivoire na daidaita matsayin diplomasiyyarta a duniya bisa hanyar karfafa yawan ofisoshin jakadancinta a kasashen duniya, in ji hukumomin kasar a ranar Litinin.

A cewar faraministan kasar Cote d'Ivoire, Daniel Kablan Duncan, wani shirin daidaita diplomasiyya, an sanya hannu kan sa a yayin taron ministoci domin karfafa yawan ofisoshin jakadancin Cote d'Ivoire a kasashen duniya da kashi 90 cikin 100 bisa ga kashi 50 cikin 100 da ake da shi a halin yanzu.

Mista Duncan ya yi wannan sanarwa a ranar Asabar da ta gabata a Grand-Bassam dake da nisan kilomita 30 daga kudu maso gabashin birinin Abidjan a yayin wata liyafar da aka shiryawa mambobin diplomasiyyar kasashen waje dake zaman wakilci a kasar Cote d'Ivoire, mambobin gwamnatin kasar da kuma tsoffin jakadun kasar Cote d'Ivoire, in ji wata sanarwar fadar faraministan kasar da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kofinta.

A cewar wannan majiya, faraminista Duncan ya jaddada muhimmancin kara karfafa dankon abokantaka tsakanin kasashen duniya, kungiyoyin kasa da kasa da kasar Cote d'Ivoire, tare da nuna maraba ga sabbin jadadun kasashen waje goma sha hudu da suka samu wakilci a kasar Cote d'Ivoire a shekarar 2013.

A yayin bikin murnar sabuwar shekara, a ranar 6 ga watan Janairu a gaban jakadun kasashen waje dake Cote d'Ivoire, shugaban kasar Alassane Ouattara ya bayyana niyyarsa ta kara karfafa huldar diplomasiyya tare da akalla kasashe 175 maimakon kasashe 94 dake hulda da kasarsa bisa kasashe 194 mambobin MDD. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China