in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha ta kori jami'an diplomasiyya na Poland da Jamus a matsayin mai da martini
2014-11-18 10:21:36 cri

Kasar Rasha ta tabbatar a ranar Litinin da korar wani gungun jami'an diplomasiyya na kasashen Poland da Jamus bisa matakin da hukumomin Moscow suka kimmanta da matakan mayar da martani. Hukumomin Poland sun dauki wani matakin da ya sabawa zaman abokantaka, da kuma rashin ma'ana. Dalilin wannan ne, Rasha ta dauki matakan mayar da martanin da ya dace, in ji ministan harkokin wajen kasar Rasha a cikin wata sanarwa, tare da kara bayyana cewa, jami'an diplomasiyyar Poland har sun riga sun bar kasar Rasha. Moscow da Warsaw ba su bayyana adadin yawan jami'an diplomasiyya da suka sallama tsakaninsu ba, sai dai kuma wasu kafofin cikin gida na Rasha sun yi tsokacin cewa, an kori wasu masu ba da shawara kan harkokin soja uku na Poland da wani ma'aikacin sashen siyasa da wannan mataki ya shafa. A ranar Jumma'a, Moscow ya baiwa jami'an sa'o'i 48 da su fice daga kasar Rasha. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China