in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha za ta baiwa Kamaru tallafin soja da fasaha domin yaki da Boko Haram
2014-06-06 09:36:52 cri

Bayan Faransa, Ingila, Amurka da Canada, kasar Rasha ma ta bayyana cewa, a shirye take wajen baiwa Kamaru tallafin soja da kayayyaki domin yaki da kungiyar Boko Haram da ta karin suna ta hanyar kai hare-hare da garkuwa da mutane a yankunan da kasar take raba iyaka da Najeriya, in ji mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha, mista Mikhail Bogdanov a ranar Alhamis a yayin wata ziyararsa a birnin Yaounde.

A shirye muke na hada karfi da karfe tare da kasashen Kamaru da Najeriya domin yaki da kungiyar Boko Haram, in ji mista Bogdanov a yayin wani taron manema labarai, bayan kammala dandalin tattaunawa tsakanin Kamaru da Rasha karo na goma wanda aka hada da bikin cikon shekaru 50 da huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha, bai ba da karin haske ba kan irin tallafin da aka shirin baiwa Kamaru da makwabciyarta Najeriya wajen murkushe Boko Haram da ke kawo babbar barazana a shiyyar yammacin Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China