Shugaba Paul Kagame na Rwanda ya nada tsohon ma'aikacin gwamnati kuma ministan kwadago, Anastase Murekezi a matsayin sabon firaministan kasar.
Sabon firaministan ya mika godiyarsa ga shugaba Kagame bisa amincewar da ya ke da shi a kansa, inda ya nada shi bisa ga wannan mukami, kana ya bayyana kudurinsa na sauke nauyin da aka damka masa tare da bayar da gudummawarsa ga ci gaba kasar ta Rwanda.
Bisa tsarin mulkin kasar Rwanda, shugaban kasar ne ke da ikon nada firaminista da kuma baki dayan 'yan majalisar zartaswar kasar. (Ibrahim)