in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabbin arangama a Benghazi sun hallaka mutane 10
2014-10-30 13:47:54 cri

An kashe mutane 10 a wani mummunan artabu da aka yi a sassa dabam-dabam na titunan gabashin birnin Benghazi dake kasar Libya, tsakanin sojojin Libya da kuma rukunonin kungiyoyin Islama masu dauke da makamai.

Wata majiya ta bayyana cewar, a jiya Laraba, an kai gawawwaki na mutane 10 zuwa cibiyar kiwon lafiya ta Benghazi a sakamakon gumuzun da aka tabka a kan titunan Benghazi, wannan adadi ya haura zuwa 201, tun bayan da sojojin masu biyayya ga Manjo Janar Khalifa Haftar mai ritaya suka fara aiwatar da hare-hare a tsakiyar watan Oktoba, domin kaddamar da yakin kwace Benghazi daga hannun 'yan tsageran islama.

Tun dai daga safiyar Laraba ne wasu rukunin sojoji masu goyon bayan Mabiya Haftar suka yi bata kashi da kungiyoyin Islama a kokawar da suke yi na kama madafun iko a sassa dabam-dabam na Benghazi.

Wadanda aka yi abin a kan idanun su sun ce, sojoji sun mamaye sassa dabam-dabam na birnin Benghazi, inda 'yan kungiyoyin Islama suka yi kakagida.

An dai yi ta fadace-fadace da makamai dabam-dabam a lokacin dauki ba dadin da aka yi a Benghazi. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China