in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin Shell ya bayyana mawuyacin hali a Najeriya bayan barna kan bututun mai
2013-09-24 12:37:04 cri

Kamfanin hakar mai na Royal Dutch Shell ya bayyana a ranar Litinin wani mahwuyacin hali a kan gine-ginensa na Bonny Light dake kudancin Najeriya bayan ya gano da matsalar yoyon mai a kan bututunsa

Kimanin ganguna mai dubu 150 na man fetur da cuba miliyan 14 na gas ake jigilar su ta wadannan bututu, in ji kakakin kamfanin Shell na Najeriya (SPDC), mista Precious Okolobo a cikin wata sanarwa a birnin lagos.

Wannan mawuyacin hali na bayyana cewa, babban kamfanin ba zai iyar cika wasu alkawuran da ya dauka na fitar da man fetur ba sakamakon wannan babban al'amarin da ya abku ba zato.

Kamfanin ya bayyana cewa, ya dauki wannan mataki bayan ya rufe bututun man dake ratsa jihar Neja wato Trans Niger Pipeline (TNP) bayan wasu sabbin matsalolin satar mai da suka janyo yoyon mai a yankunan Bodo na yammaci da Oloma.

Bututun TNP na kasancewa abin kaiwa hari, kuma an rika rufe shi har sau biyar tun daga farkon watan Yuli bisa dalilin yawan yoyon da ake samu dake da nasaba da satar mai, in ji wannan kamfanin Shell.

Haka zalika, Shell ya bayyana cewa, yana aiki sosai domin gyara bututun da kuma sake amfani da shi tun da wur wuri.

Kamfanin man fetur din na nuna damuwarsa sosai kan yawan sacen mai dake karuwa a cikin wannan yanki na Neja Delta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China