A halin da ake ciki, shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya shaidawa Sarki Abdullah na kasar Saudi Arabia ta wayar tarho cewar, ya daura damarar yaki da 'yan tsagerar kasar musulunci IS.
Buga wayar da Obama ya yi zuwa ga sarki Abdullahi, ta zo ne gab da 'yan awowi kadan kafin ya gabatar da jawabinsa ga Amurkawa da kuma duniya baki daya, a kan barazanar dake tattare da mayakan kasar musulunci.
A yayin tattaunawar da suka yi, shugabannin biyu sun tatttauna a bisa damuwar da suke da ita ta barazanar mayakan kasar musuluncin, kuma sun tattauna a game da bukatar dake akwai na inganta bayar da horo da makamai ga 'yan adawar Syria masu sassaucin ra'ayi.
A cikin jawabin nasa a jiya Laraba, Obama ya ce, za su samar da cikakkun matakai wadanda za su karya, tare da murkushe kasar musuluncin.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, tuni ya isa yankin Gabas ta Tsakiya domin samun goyon bayan kokarin da Washington ke yi na samar da hadin kai a yankin, kuma tuni aka shirya wata ganawa a birnin Jeddah dake Saudi Arabia, tsakanin John Kerry da takwarorinsa daga kasashen Larabawa 10 da Turkiyya. (Suwaiba)