Rahotanni daga jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya na cewa, mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon harin bam da wani 'dan kunar bakin ya kaddamar a jiya Litinin.
Shaidun gani da ido sun ce, maharin ya tada bam din ne a birnin Potiskum cikin dandazon jama'a, dake jerin gwano yayin wani taron addini na mabiya akidar Shi'a.
Wani mazaunin birnin wanda ya shaida wa kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua yadda lamarin ya wakana, ya ce, mai yiwuwa ne adadin wadanda suka rasa rayukansu yayin harin ya kai mutane 30.
Shi kuwa a nasa bangare, kwamishinan 'yan sandan jihar tabbatar da aukuwar lamarin ya yi, yana mai cewa, maharin na cikin wadanda suka rasa rayukansu. Ko da yake dai bai tabbatar da adadin wadanda suka rasu ba.
Kafin dai harin na Litinin birnin na Potiskum ya samu farfadowa ta fuskar tsaro, tun bayan harin watan Yuni da maharan kungiyar Boko Haram suka kaddamar a wasu masallatan birnin.
Tuni dai jami'an tsaro suka yi wa yankin da lamarin ya faru kawanya, domin kare aukuwar karin wasu hare-haren. (Saminu)