A sakamakon sauka daga kan mulki da shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore ya yi, a halin da ake ciki shugabannin Afrika ta yamma gudan uku sun ziyarci kasar ta Burkina Faso, domin su taimaka mata komawa kan turbar mulkin farar hula bayan da sojoji suka karbe iko a kasar.
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama, wanda shi ne shugaban kungiyar tattalin arzikin Afrika ta yamma ECOWAS da shugaban kasar Nigeria Good Luck Jonathan da shugaban kasar Senegal Macky Sall tuni suka isa Burkina Faso, inda suka gana da shugaban soji na rikon kwarya na kasar, tare da yi mashi kashedi da a mika mulkin kasar a hannun farar hula.
Ana sa ran wakilan kasar daga bangaren sojoji da 'yan siyasa da shugabannin addini za su zabi 'yan takara guda 3, kafin a sami daidaito a game da gwamnatin rikon kwarya a kasar.
Shi dai tsohon shugaban kasar, an tilasta masa sauka ne daga karagar mulkin kasar bayan ya shafe shekaru 27 yana mulki a yayin da masu zanga-zanga suka cika tituna, domin nuna kin amncewa da matakin da ya so dauka na canza kundin tsarin mulki domin kara karfafa mulkinsa. (Suwaiba)