A kalla maharan kungiyar Boko Haram 42 ne aka kashe a wani dauki ba dadi da sojojin Nigeriya lokacin da harin da suka kai ya ci tura a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nigeriya, kamar yadda wani jami'in tsaro ya bayyana a ranar Asabar din nan.
Maharan a kan babura da wata motar a kori kura ta hilux sun farma kauyen Sabon Gari ne dake kusa da Biu mai tazaran kilomita 189 daga Maiduguri, babban birnin jihar a ranar Jumma'an nan da ta gabata, amma suka gamu da cikas daga wajen sojojin Nigeriya wadanda daman suke isa wurin kafin maharan bisa ga bayanan sirri da suka samu.
Wannan jami'in tsaron ya shaida wa Xinhua cewa, sojojin kasar sun koya wa mazauna kauyen yadda za su kare kansu kafin a kawo masu agaji ta hada kungiyar 'yan banga da galibinsu matasa ne, don haka suka jimma maharan lokacin da suka kawo hari.
Wani mazaunin yankin Audu Uba matashi 'dan kungiyar 'yan banga a garin Biu ya tabbatar da faruwar hakan, yana mai bayanin cewa, rundunar sojin kasar a wannan yankin sun fatattakin maharan wadanda suka tsere zuwa wassu kauyuka dake kusa, inda a nan ne kuwa aka kame su aka kashe. (Fatimah)