in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan bindiga sun hallaka mutane 17 tare da sace wasu 30 a jihar Borno
2014-10-27 10:20:56 cri

Wasu 'yan bindiga da ba a tantance su ba, sun hallaka mutane 17, suka kuma yi awon gaba da wasu matasa kimanin 30 daga kauyukan dake yankin karamar hukumar Maffa a jihar Borno.

Mayanakan dai sun farwa yankin na Maffa mai makwaftaka da garin Gamboru, kusa da iyakar Najeriya da Kamaru ne tsakanin ranekun Alhamis zuwa Asabar, lamarin da ya sabbaba kisan fararen hula da dama. Rahotanni daga karamar hukumar ta Maffa dai na cewa, da dama daga al'ummar yankin sun tsere zuwa birnin Maiduguri domin tsira da rayukansu da iyalansu.

Da dama dai daga matasan da 'yan bindigar suka kwashe zuwa sansanin su 'yan kimanin shekaru 13 ne zuwa sama.

Cikin watan Agustan da ya gabata ma dai dakarun sojin Najeriyar sun shafe tsahon lokaci su na fafata da mayakan kungiyar Boko Haram, a wani yunkuri na hana mayakan mamaye yankin na Maffa. Ko da yake dai kawo yanzu mahukunta ba su tabbatar da ko 'yan Boko Haram din ne suka mamaye yankin ba.

Har kawo wannan lokaci 'yan Boko Haram din na tsare da 'yan mata sama da 200, da suka yi awon gaba da su daga makarantar Chibok a jihar ta Borno tun cikin watan Afirilun da ya shude. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China