A cewar Mista Ye, zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta harba taurarin dan Adam na gwaji a karkashin tsarin na BDS guda 4, gami da taurarin BDS na tallafawa aikin sufuri guda 16, ta haka an kammala mataki na 2 na aikin gina tsarin BDS, wato kafa wata yanar taurarin dan Adam.
Mista Ye ya kara da cewa, a bisa shirin da aka tsara, zuwa shekarar 2020, za a kammala aikin gina tsarin BDS da ya kunshi taurarin dan Adam guda 35, wanda hakan zai iya tabbatar da wurin na'urorin sufuri suke, da ba da jagora ga jirage, gami da daidaita lokacin agogo.
Ya zuwa karshen shekarar 2011, an riga an kafa wani tsarin BDS na yanki, wanda ke samar da hidima ga kasar Sin, da yankunan dake kewayen kasar.(Bello Wang)