Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, wata rokar dakon kayayyaki maras matuki ta kama da wuta, ta kuma tarwatse 'yan dakikoki kadan da harba ta sararin samaniya.
Kafar talabijin ta NASA ta nuna bidiyon fadowar roka mai dauke da kayan bincike ta wani kamfani mai zaman kansa a gabashin jihar Virginia. Babu dai wani mutum da wannan hadari ya ritsa da shi.
Tuni kuma kamfanin Orbital dake mallakar rokar ya alakanta faduwarta da tangardar na'ura, ya kuma alkawarta yin karin haske game da hakan a nan gaba.
Kafin fadowarta, roka mai suna Cygnus, na dauke ne da kayayyakin bincike da suka kai nauyin kilogiram 2,290, wadanda aka tsara kaiwa wata tashar saukar kumbuna ta sararin samaniya. (Saminu)