in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Obama ya yi alkawarin hada kai da majalisar dokokin kasarsa
2014-11-06 15:34:16 cri

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da 'yan jam'iyyar Republicans na kasar bayan da suka lashe zaben da aka yi a kasar, hakan ya sa sun doke jam'iyyar Democrats, a yayin da suka zamanto jam'iyya mafi rinjaye a cikin majalisun dokokin kasar guda biyu.

A yayin wani taron manema labarai a fadar White House, Obama ya ce, a bisa dukkan alamu 'yan jam'iyyar Republicans sun lashe zaben tsakiyar shekara, to amma ya yi amanna cewar, masu kada kuri'a har yanzu zuciyarsu tana tare da 'yan jam'iyyarsa ta Democrats.

Obama ya ce, yana sa rai ya yi aiki tare da 'yan jam'iyyar ta Democrats a kuma daidai lokaci guda, Obama ya yi wa shugaba mafi rinjaye a babbar majalisar dokokin kasar Mitch McConnell farin cikin zabar shi da aka yi.

Obama ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da garambawul a bangaren shigi da ficin kasa, duk kuwa da adawar da yake fuskanta daga 'yan jam'iyyar Republicans.

Shugaba Obama ya kuma bukaci majalisar dokokin kasar da ta dauki mataki na samar da kudade a cikin gagggawa domin dakile cutar Ebola da kuma yaki da 'yan ta'addan IS. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China