Jagoran gwamnatin rikon kwaryar kasar Burkina Faso Laftana Kanal Isaac Yacouba Zida, ya bayyana aniyarsa ta mika ragamar kasar ga farar hula.
Sarkin masarautar Mossi, wanda ke matsayin daya daga masu fada-a-ji a kasar Mogho Naba ne ya tabbatar da hakan, bayan ganawarsa da Kanar Zida. Sai dai kawo yanzu Zidan bai yiwa manema labaru karin haske game da wannan batu ba.
Kafin hakan, a ranar Litinin kanal Zida ya bayyana wa duniya cewa, gwamnatin rikon kwaryar da yake jagoranta za ta gudana ne bisa doron doka da oda, karkashin kuma ikon daukacin masu ruwa da tsaki daga dukkanin sassan kasar.
Kanar Zida ya haye ragamar jagorancin kasar ne bayan amincewar da ya samu daga sassan dakarun sojin kasar, biyowa bayan murabus din shugaba Blaise Compaore a Juma'ar karshen makon jiya.
Shugaba Compaore ya fuskanci bore daga al'ummar Burkina Faso ne sakamakon yunkurin da ya yi na zarcewa a kan mulki, bayan shafe shekaru 27 yana shugabancin kasar. (Saminu)