in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe 'yan ta'adda 13 a wani hari a Nigeriya
2014-09-23 10:01:05 cri

Rahotannin da kamfanin dillanci labarai na kasar Sin Xinhua ya samo na nuna cewa, an kashe a kalla mutane 13 da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne a lokacin wani musayar wuta tsakanin su da sojojin Nigeriya a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar, kamar yadda wani jami'in soji ya tabbatar a ranar Litinin din nan.

Rundunar sojan Nigeriyan dai sun kai mamaye ne bayan da wadanda ake zargin 'yan kungiyar na Boko Haram ne suka buya a wata kasuwa a garin Mainok, mai nisan kilomita 56 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Jumma'a, kamar yadda wannan jami'in tsaron da ya bukaci a sakaya sunan shi ya bayyana wa Xinhua ta wayar tarho.

Tun da farko dai akwai rahotannin dake cewa, mutane fararen hula fiye da 20 sun mutu sakamakon wannan mamaye bayan da sojojin suka harba gurneti a tsakiyar kasuwar. Sai dai rundunar sojin kasar bayan samun sakon gaggawa game da shigowar wadannan 'yan kungiya cikin kasuwar sun afka mata ba tare da bata lokaci ba, inda suka fara musayar wuta, abin da nan take ya yi sanadiyar mutuwar mutane 13, daga cikin sauran kuma suka tsere da raunin bindiga.

Wani direban bas Ba'ana Gunda wanda yake zarya da fasinjoji a kan hanyar wannan kasuwa ya ce, ya zuwa safiyar ranar Litinin din nan, akwai gawawwakin mutane yashe a wannan kasuwa. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China