Kwamitin tsaro na MDD ya yi kakkausar suka a game da harin da aka kaiwa motar jakadan kasar Jordan dake Tripoli, babban birnin kasar Libya.
Rahotanni sun ce, harin ya haddasa yin awon gaba da jakadan kasar ta Jordan, tare da raunata direban shi.
Wata sanarwar da ta fito daga kwamitin tsaron na MDD, wadda aka rarrabawa manema labarai ta ce, 'ya'yan kwamitin tsaro na MDD, sun nuna matukar damuwarsu, a game da farmakin da aka kai, a inda kuma suka bukaci da'a saki jakadan kasar ta Jordan nan take.
Wasu mutane wadanda suka rufe fuskokinsu a cikin motoci biyu sun bude wuta a kan motar jakadan kasar Jordan dake Libya, Fawaz al-Etan a tsakiyar Tripoli, daura da ofishin jakadanci na Jordan a safiyar Talata, wannan bude wuta ya haifar da jikkata direban jakadan, a inda kuma masu kai harin suka yi awon gaba da jakadan, zuwa wata maboya wacce kawo ya zuwa yanzu ba'a san inda take ba, kamar dai yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen Libya ta bayyana.
Har yanzu dai ba'a da masaniyar ko su wane ne suka kai harin, kuma har yanzu ba'a gane wadanda suka sa aka yi wannan aika aika ba. Majiyoyi sun ce, har yanzu ma'aikatar ba ta sami wani sako daga mahara ba. (Suwaiba)