in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya tana son aiwatar da ka'idojin kasa da kasa domin kare masaya
2014-10-31 15:20:14 cri

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana a ranar Alhamis niyyarta ta cigaba da amfani da ka'idojin kasa da kasa domin kare masaya, tare da nuna cewa, kasar dake yammacin Afrika ta gabatar da sauye-sauyen ta fuskar shari'a, da kuma dabarun siyasa domin karfafa matakan kare masaya.

Joseph Odumodu, darektan janar na ka'idojin kasa na Najeriya (SON), ya bayyana wannan niyya a yayin wani taron manema labarai a birnin Lagos, cibiyar tattalin arzikin kasar, bisa tsarin bukukuwan karama ranar ma'aunin kasa da kasa a Najeriya.

Kasar Najeriya ta bayyana niyyarta wajen karfafa matakin kare masaya da kuma kafa wani tsarin ma'aunin kasa, tare da ba da hadin gwiwa tare da gamayyar kasa da kasa, in ji mista Odumodu tare da bayyana cewa, hadin gwiwa tare da gamayyar kasa da kasa na da muhimmancin gaske, ganin yadda ayyukan jari hujja, da kuma yadda kasuwancin yau da kullum ke shiga zamani. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China