Kasar Amurka ta yi tayin bayar da ladan dala miliyan 45 ga duk wanda ya taimaka da bayanai game da wasu jiga-jigan shugabannin reshen kungiyar Al-Qaeda 8 da ke yankin kasashen Larabawa (AQAP).
Ma'aikatar harkokin wajen kasar wadda ta bayyana hakan ranar Talata ta ce, shirin harkokin shari'a na ma'aikatar ya ware ladan dala miliyan 10 ga duk wanda ya taimaka da bayanai da za su taimaka wajen damke Nasir al-Wahishi, shugaban kungiyar ta AQAP, yayin da za a bayar da ladan dala miliyan biyar-biyar kowanne ga duk wanda ya taimaka da bayanai game da sauran shugabannin kungiyar guda 7.
Kungiyar ta AQAP dai ta sha kaddamar da hare-haren ta'addanci kan gwamnatin Yemen, Amurka da sauran kawayenta da ke ketare, ciki har da harin kunar bakin waken watan Mayun shekara ta 2012 da aka kai a Sanaa, babban birnin kasar, wanda ya halaka sama da mutane 100.
Idan ba a manta ba, barazanar kungiyar ta AQAP ta tilastawa Amurka rufe ofisoshin jakadancinta sama da 20 na wani 'dan lokaci a shekara ta 2013. (Ibrahim)