in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu fursunoni 230 sun tsere daga gidan yarin Nord-Kivu dake DRC
2014-10-20 10:55:47 cri

Fiye da fursunoni 230 ne suka tsere a ranar Asabar da yamma daga babban gidan yarin Kakwangura a Butembo, yankin dake kusa da kilomita 300 daga arewacin Goma, babban birnin gundumar Nord-Kivu, a gabashin kasar DRC-Congo, in ji wasu majiyioyin hukumomin kasar. Magajin garin rikon kwarya na Butembo, Godefroid Matimbya, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, lamarin ya faru a yayin da wasu mutanen dauke da makamai da ba'a tantance ba suka kai harin kan ginin gidan yarin. Mutane ishirin da tara da suka tsere, jami'an tsaro sun kamo su. A cewar majiyoyin jami'an gidan yari, gidan yarin Kakwangura na dauke da fursunoni kimanin 324. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China