Mataimakin shugaban kasar Sin Li Yuanchao, ya jagoranci mika wasu kayayyakin aiki ga hukumar TAZARA, mai lura da harkar sufurin jiragen kasa ta kasar Tanzania. Wadannan kayayyakin dai na karkashin wani shirin samar da bashi na musamman, wanda Sin ta daddale da kasashen Zambia da Tanzania.
An dai gudanar da bikin gabatar da wadannan kayayyaki ne, da suka hada da kungiyar daga kayayyaki guda 4 ga hukumar ta TAZARA, yayin ziyarar aiki ta kwanaki 6 da Mr. Li ke gudanarwa a kasar ta Tanzania.
Daga bisani mataimakin shugaban kasar ta Sin ya hau daya daga jirajen kasan hukumar zuwa Yombo dake wajen birnin Dar es Salaam, inda ya bayyana gamsuwa ga yadda aka kyautata kula da layin dogon, wanda aka gina shekaru sama 40 da suka gabata.
Har ila yau Mr. Li ya alkawarta tattaunawa da sauran jami'an kasar Sin da zarar ya koma gida, domin kara fidda hanyoyin tallafawa kasar ta Tanzania.
A nasa tsokaci yayin da yake karbar kayan aikin a madadin TAZARA, ministan ma'aikatar sufurin kasar Harrison Mwakyembe, cewa ya yi wannan tallafi daya ne daga alkawarun da Sin ta yi wa kasarsa a baya. Daga nan sai ya bayyana burin mahukuntan Tanzania na martaba dukkanin taimako da Sin ke daukar nauyi bayarwa ga kasarsa tun daga shekarun 1970 kawo yanzu. (Saminu)