Shugaban asusun kula da kariyar namun daji na duniya WWF Yolanda Kakabadse ya baiwa kungiyar kula da namun daji ta Tanzania kyautar yabo da aka yiwa lakabi da "shugabannin kariyar namun daji na duniya".
Kungiyar kariyar namun dajin ta Tanzania da aka yi wa lakabi da "19 WMAs" wato 19 Wildlife Management Areas ta samu kyautar yabon ne a sakamakon gagarumar nasarar da ta samu a wajen kare namun dajin wadanda ke cikin barazanar karewa da kuma kokarin da take yi na kariyar gandun dajin da namun daji ke zama.
Kungiyar kariyar namun dajin ta Tanzania tana kulawa da wasu wurare da aka kare a wasu kauyuka 146, masu girman da ya kai murabba'in 28,389, wanda kuma akwai jama'a dubu 410 dake zaune a kauyukan wadanda kuma kungiyar tana aiki da su domin kariyar namun dajin, kuma jama'ar su ma suna samin abin masarufi a sakamakon gudumuwar da suke badawa a wajen kariyar namun dajin. (Suwaiba)