in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci 'yan tawayen Sudan ta Kudu da su martaba yarjejeniyar tsagaita bude wuta
2014-05-16 10:49:31 cri

A ranar Alhamis ne gwamnatin kasar Sudan ta yi kira ga sassa biyu da ke fada da juna a kasar Sudan ta Kudu, da su yiwa Allah su martaba yarjejeniyar tsagaita bude wutan da suka cimma, ta hanyar dakatar da fada, tare da barin a kai kayan agaji ga mutanen da ke bukata.

Wannan kiran na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sudan ta bayar, inda ta sake yin kira ga sassan biyu da ke gwabza fada da juna da su martaba yarjejeniyar da suka sanya wa hannu a kai a ranar 9 ga watan Mayu.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, fada ya barke a jihar Upper Nile mai arzikin mai tsakanin dakarun gwamnati da na magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar, ko da yake babu rahoton wadanda suka jikkata, amma rikicin da ke faruwa a Sudan ta Kudu ya yi tasiri sosai kan dukkan kasashen da ke yankin, musamman kasar Sudan.

Idan ba a manta ba, a ranar 9 ga watan Mayu ne 'yan tawayen kasar Sudan ta Kudu suka sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaida bude wuta a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda suka ayyana tsagaita wuta tare da kafa gwamnatin wucin gadi, ta yadda za a shirya gudanar da zabe a kasar cikin shekara daya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China