in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 15 a Najeriya
2014-09-18 10:44:55 cri

Rundunar 'yan sandan jihar Kano dake arewa maso yammacin Nigeria ta ba da tabbacin cewar, wasu mutane 15 sun rasa rayukansu, ciki har da wasu mutane biyu da suka kai harin kunar bakin wake a kan kwalejin ilmi ta tarayya dake Kano a jiya Laraba.

kwamishinan 'yan sanda na jihar ta Kano Aderinle Shinaba ya bayar da tabbacin abkuwar hakan a yayin da yake jawabi ga 'yan sanda jim kadan bayan ya ziyarci kwalejin inda abin ya faru.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce, wasu mutane 34 da suka hada da dalibai da malaman kwalejin sun samu raunuka dabam-dabam a sakamakon harin da aka kai, kuma ya ce, tun kafin maharan su kutsa kai cikin makarantar, sai da suka yi dauki ba dadi da masu gadin makarantar, inda hakan ya haifar da musayar wuta a tsakanin su.

Kamar yadda ya ce, daya daga cikin masu gadin makarantar ya samu galabar kai harbi a kan daya daga ciki maharan wanda ke dauke da bama-bamai, kuma nan take bayan harbin bam din da yake dauke da shi, ya tashi ya hallaka shi har lahira.

Duk da yake cewar, babu wata majiya da ta fito karara ta dauki nauyin aiwatar da wannan farmakin da aka kai da bam a kan kwalejin, to amma mazauna birnin Kanon suna zargin 'yan kungiyar Boko Haram da aiwatar da harin, musamman da yake 'yan kungiyar ta Boko Haram sun kasance suna daukar nauyin aikata duk wani hari da sace jama'a da aka yi a Nigeria tun daga shekarar ta 2009. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China