in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Najeriya ta amince da karbar rancen dala biliyan 1 domin yaki da Boko Haram
2014-10-23 10:45:02 cri

Majalisar wakilan Najeriya ta amince a ranar Laraba, da bukatar shugaba Goodluck Jonathan na neman rancen kudi na a kalla dalar Amurka biliyan daya domin yaki da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta. Majalisar dattijan Najeriya ta amince a ranar 25 ga watan Satumba da bukatar shugaban Najeriya na karbo rancen wannan adadi domin yaki da matsalolin tsaron kasa. Majalisar da farko ta kira ministar kudi madam Ngozi Okonjo-Iweala gaban kwamitin 'yan majalisu dake kula da harkokin kudi da taimako, domin ta kara ba su karin haske kan matakai da sharudan wannan rance. 'Yan majalisun sun kuma bukaci mashawarcin kasa kan tsaro da ya gabatar musu bayanin kan kudaden da ake kebe wa rundanar sojojin sama, da na kasa, da na ruwa, ga ma'aikatun gwamnati da kuma 'yan sandan Najeriya.

Wadannan matakai, an dauke su ne a yayin binciken rahoton kwamitocin dake karkashin jagorancin 'dan majalisa Adeyinka Ajayi game da harkokin kudi da taimako, bayan shawarwarin rahoton kwamitocin hadin gwiwa.

Shugaba Jonathan ya bukaci a cikin watan Yuli ga majalisar dokokin kasa da ta amince da karbar wani rancen dalar Amurka biliyan daya domin yaki da kungiyar Boko Haram. A cikin wata wasikar da ya aike wa shugaban majalisar dattijan Najeriya, David Mark, shugaban Najeriya ya tabo wajabcin karbo wani rance daga waje domin kyautata tsarin tsaro da samar da kayayyakin tsaro, ta yadda za'a samu sukunin yaki da barazanar Boko Haram dake gurgunta cigaban Najeriya, musammun ma a arewacin kasar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China