Kungiyar tarayyar hadin kan kasashen Afrika AU ta shawarci Burkina Faso da ta mika mulkin ragamar kasar a hannun farar hula a cikin makonni 2.
Hukumar samar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar tarayyar hadin kan Afrika mai mambobi 54, ta gudanar da taronta a babbar hedkwatar AU dake Addis Ababa, a game da halin da ake ciki a Burkina Faso.
A yayin da ya shugabanci taron, Simeon Oyono Esono, wanda shi ne wakilin kasar Equatorial Guinea na din-din-din a kungiyar ta AU ya shaida wa manema labarai cewar, taron ya tattauna matsalolin dake addabar kasar ta Burkina Faso tare da ba da umurni na mika mulki a cikin makonni biyu.
Nkosazana Dlamini Zuma, shugabar kungiyar tarayyar ta Afrika ta yi kira a kan 'yan siyasa masu fada a ji da masu kare hakkin bil'adama a Burkina Faso da su yi aiki tare domin samun daidaito na mika mulki a hannun farar hula, tare da gudanar da zabe a cikin 'dan kankanen lokaci. (Suwaiba)