Sojoji a Burkina Fasa sun tarwatsa dubban masu zanga-zanga, tare da tilasa musu ficewa daga harabar gidan talabijin mallakar kasar, bayan da masu boren suka kame harabar na dan wani lokaci.
Rahotanni sun ce, sojojin sun rika harba bindigogi sama domin tsorata masu boren a wani yunkuri na korar su, tare da dakile yunkurin da jagorar jam'iyyar PDC Saran Sereme ta yi, na ayyana kan ta a matsayin shugabar gwamnatin rikon kwaryar kasar a jiya Lahadi.
Kaza lika sojojin sun sanya shingaye domin hana jama'a sake taruwa a babban filin dake tsakiyar birnin Ouagadougou, filin da ya zamo matattarar jama'a yayin zanga-zangar makon jiya.
Ana ci gaba da samun sabani tsakanin manyan masu da'awar jagorantar kasar a yanzu haka, wadanda suka hada da babban hafsan sojin kasar Nabere Traore, da babban dogarin hambararren shugaban kasar Isaac Zida. Yayin da kuma a hannu guda wasu ke kira ga mika ragamar gwamnatin rikon kwaryar ga farar hula.
A wani cigaban kuma Amurka ta yi Allah wadai da yadda sojojin kasar ta Burkina Faso ke kokarin kakabawa al'ummar kasar ra'ayin kashin kai. Wata sanarwa da sakatariyar cikin gidan Amurkan Jen Psaki ta fitar ta ce, kamata ya yi sojojin su girmama kundin mulkin kasar, su kuma gaggauta daukar matakan gudanar da zabe cikin adalci, ba kuma tare da wani bata lokaci ba. (Saminu)