A yau Asabar ne manyan sojojin kasar Burkina Faso suka amince da dogarin fadar shugaban kasar Laftana kanar Issac Zida ya jagoranci gwamnatin rikon kwaryar kasar, bayan da aka tilastawa tsohon shugaban kasar Blaise Compaore sauka daga mukaminsa a ranar Jumma'a.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sojojin kasar suka bayar, bayan ganawar manyan sojojin kasar a yau Asabar, inda suka amince baki dayansu da zabar kanar Zida a matsayin jagoran gwamnatin wucin gadin kasar.
A ranar Alhamis ne daruruwan dubban jama'a suka fito kan titunan babban birnin kasar, inda suka hana 'yan majalisar dokokin kasar kada kuri'ar yiwa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarimar da za ta baiwa shugaba Blasie Compaore mai shekaru 63 damar yin wani karin wa'adin mulki. (Ibrahim)