Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta yi kiran da a samar da gwamnatin farar hula, tare da mika mulkin bisa ga bukatun al'umma a kasar Burkina Faso.
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar mai mambobi kasashe 54 zai kira taro a ranar Litinin din nan domin duba yanayin da ake ciki a kasar kamar yadda wata sanarwa daga kungiyar ta fitar a ranar Asabar din nan.
Madam Nkosazana Dlamini-Zuma, shugabar kungiyar gudanarwa ta AU tana ci gaba da sa ido sosai game da abin da ke faruwa a kasar, kamar yadda sanarwar ta yi bayani. Haka kuma Madam Zuma ta yi kira ga masu ruwa da tsaki na siyasar kasar da kungiyoyi masu nasaba da hakan da su yi aiki tare domin cimma matsaya, da kuma sauke nauyin dake rataye bisa wuyansu, abin da zai kai ga cimma matsaya game da samar da gwamnatin farar hula ba tare da bata lokaci ba, sannan a yi babban zabe cikin walwala, gaskiya da kuma a bayyane.
Ta jaddada shirin kungiyar a ko da yaushe na aiki kafada da kafada da kungiyar tarayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afika ECOWAS da MDD wajen ba da goyon baya ga al'ummar Burkina Faso da daukacin masu fada a ji a siyasa da zamantakewar kasar, sannan kuma za ta ba da gudunmuwarta wajen wayar da kan jama'a game da taimakon da suke bukata daga ciki da wajen nahiyar. (Fatimah)