A kalla mutane biyar sun rasa rayukansu a wata tashar motar bas, dake unguwar sabon Gari a jihar Kano, a yayin da wani 'dan harin kunar bakin wake ya tada wasu bama-bamai a jihar dake arewa maso yammacin Nigeria.
Kakakin 'yan sandan jihar Kano Musa Majiya, wanda ya tabbatar da abkuwar hakan ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce, tuni rundunar 'yan sandan jihar ta aike da 'yan sanda masu kwance bam da kuma masu kwantar da tarzoma, zuwa inda aka kai harin.
To amma kakakin 'yan sandan ya ki ya ce uffan a game da takamaiman adadin, wadanda suka sami rauni, sai dai wasu shedu da a kai harin a idanunsu sun ce, a kalla mutane 10 sun sami rauni. Shedun sun ce, bam din ya tashi a yayin da fasinjoji ke niyyar shiga mota zuwa kudancin Nigeria.
Shekara biyu da suka wuce, an taba kai irin wannan harin, a tashar motar da a kai harin na yanzu, a inda a wancan lokacin, mutane da yawa suka rasa rayukansu, kuma wasu mutanen da dama suka jikkata.
Har yanzu dai ba'a san ko wace kungiya ce ta aiwatar da harin na jiya Alhamis ba. Shekaru biyu da suka wuce dai, kungiyar Boko Haram ce ta kai wancan harin na farko da aka kai a tashar. (Suwaiba)