Ministan tsaron kasar Ukraine, Valeriy Geletey ya nuna a ranar Litinin cewa, rikici tsakanin sojojin gwamnatin kasar da mayakan 'yan aware masu neman 'yancin gabashin Ukraine ya dauki wani sabon salon a yaki.
Mista Geletey ya zargi kasar Rasha da fara mamaye wasu yankunan kasarsa, tare da bayyana kawo karshen ayyukan sojojin gwamnati a gabashin kasar.
Ayyukan sojojin gwamnati da suka shafi kwato gabashin Ukraine daga hannun 'yan ta'adda sun kare. Ya zama wajibi mu yi aiki cikin gaggawa domin kare kasarmu daga Rasha, in ji wannan jami'i.
Haka kuma ministan ya zargi Moscou da alhakin tashen-tashen hankalin dake faruwa a yankunan Lougansk da Donetsk, tare da tabbatar da cewa, Rasha, ta wasu hanyoyin da ba'a tabbatar ba na bayyana barazanarta na amfani da makaman nukuliya na sabon salo kan kasar Ukraine. (Maman Ada)