in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 7 suka samu rauni yayin harin gurnet a gari kan iyaka a Kenya
2014-06-12 12:28:06 cri

Mutane 7 ne suka jikkata a wani hari da aka kai da gurnet a garin Garissa, dake arewacin Kenya, kamar dai yadda kwamandan 'yan sanda na karamar hukumar Garissa, Charles Kinyua ya bayyana.

Kinyua ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, bayan wani kara mai karfi, na fashewar gurnet da karfe bakwai da rabi da yamma, sai wasu fararen hula su 7, wadanda ke hira a kofar gidajensu dake titin Ngamia na garin Garissa, suka samu rauni, kuma kamar yadda ya ce, an kai asibiti da sauri da wadanda harin ya rutsa da su.

Kinyua ya ce, mutanen da aka kaiwa harin sun ba da rahoto cewar, wanda ya kai harin mutum guda ne, bayan ya boye a duhu, ya jefa masu gurnet. Kinyua ya ce, 'yan sanda suna zargin cewar, maharin ya yi niyyar ya kashe wadanda ya kaiwa harin, to kuma sai suka yi sa'a suka tsira, saboda gurnet din bai same su ba kai tsaye.

Wannan harin ya biyo bayan kashe wani babban malamin addinin musulunchi Sheikh Abdirashid, wanda wasu da ba'a san ko su wane ne ba suka harbe shi kafin mako guda da ya gabata. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China