in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Libya ta fara tattaunawa da kungiyoyin 'yan adawa
2014-09-30 09:55:11 cri

Majalisar dokokin kasar Libya ta fara tattaunawa da jiga-jigan 'yan siyasa a garin Ghadames da ke kan iyaka, a kokarin hana kasar tsunduma cikin mummunan rikici.

Kafofin watsa labaran kasar sun bayyana cewa, tawagogin da ke wakiltar bangarori daban-daban da ke halartar tattaunawar, za su mayar da hankali ne kan yadda za a kawo harshen munanan hare-haren da 'yan ta'adda ke kaiwa juna wadanda yanzu haka suke shafar biranen kasar daban-daban da kuma shirin mika mulki na kasar.

Ana gudanar da tattaunawar ce wadda wakilin babban sakataren MDD na musamman Bernardino Leon ya kirkiro. karkashin sa-idon tawagar MDD da ke Libya.

Bisa tsarin shirin mika mulki na kasar ta Libya, tuni dai majalisar wakilan kasar da aka zaba ta maye gurbin tsohuwar majalisar wucin gadin kasar. Ko da yake 'yan tawaye da ke dauke da makamai wadanda ke goyon bayan tsohuwar majalisar dokokin kasar, ta ki amincewa da sabuwar majalisar, matakin da ya sa ta nemi kafa nata gwammatin.

Kasar Libya dai ta fada cikin rikicin siyasa ne tun boren shekarar 2011 da ya yi sanadiyar hambarar da tsohon shugabar kasar marigayi Mu'ammar Gaddafi, lamarin da ya haifar da majalisu da gwamnatoci biyu da ke gaba da juna a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China