in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Nigeria sun kashe shugaban Boko Haram lokacin musanyar wuta
2014-09-25 10:22:37 cri

Sojojin Nigeria sun tabbatar da cewa, sun dade da kashe mutumin da ake zargin shi ne jagoran 'yan kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, kamar yadda mahukuntar tsaron kasar suka fadi a ranar Laraban nan.

Wanda ke sojan gona da sunan Shekau a cikin faya-fayen bidiyon da kungiyar ta kan fitar, sunan shi Mohammed Bashir, amma lallai shugaban nasu mai suna Shekau sun kashe shi lokacin da suka yi musanyar wuta a garin Konduga dake jihar ta Borno kamar yadda kakakin rundunar tsaron kasar Chris Olukolade ya tabbatar wa manema labarai a wata sanarwa da Xinhua ya samu.

Olukolade ya ce, 'yan ta'addan da dama da suka hada da manyan kwamandojinsu sun rasa rayukansu a lokacin wannan musayar wutan da aka dauki kusan awoyi biyar ana yi, haka kuma rundunar sojin ta kame wadansu 'yan kungiyar da dama tare da makamansu, yana mai bayanin cewa, mazauna wajen da aka addabe su da ta'addanci su ne suka hada kai da jami'an tsaron wajen samar da bayanai dangane da Abubakar Shekau din.

Kakakin rundunar tsaron ya ce, 'yan ta'adda 135 suka mika kansu tare da makamansu ga rundunar sojin a garin Biu dake jihar Borno, sannan wadansu 88 suka mika kansu a yankin Mairiga/Bun, sannan wadandu 45 aka kama su a wuraren garin Mubi dake jihar Adamawa.

Har ila yau Olukolade ya ce, dukkan 'yan ta'addan ana masu tambayoyi da bincike yadda doka ta tanada. 'Yan ta'addan, in ji shi, a ci gaba da yada bayanan da suke yi na tashin hankali, sun kuduri sake kame garuruwa dake zagaye da Maiduguri, babban birnin jihar ta Borno wanda nan ne babban burinsu.

Manazarta sun ce, wannan cigaba ya kara nuna cewa, kokarin da Nigeria take yi na yaki da ta'addanci yana kawo wa karshen shekaru kusan biyar da aka yi, ana cikin zaman fargaba da Boko Haram suka kawo, kungiyar da ta kawo babbar barazana ga tsaro a kasar dake yammacin Afrika. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China